Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan Syria

Majalisar Dinkin Duniya_ Syria
Image caption Majalisar Dinkin Duniya_ Syria

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa, ba zata iya biyan bukatun mutanen da rikicin Syria ya shafa ba.

Mai kula da ayyukan jin kai ta majalisar dinkin duniya Valeri Amos ta ce rikicin na habaka cikin hanzari na fitar hankali.

Ta ce akasarin wadanda suka alkawarta ba da kudaden agaji dala biliyan daya da rabi ba su kai ga biya ba, kuma ko da sun biya ma ba zai isa biyan bukatun mutanen ba.

Kusan kimanin mutane miliyan hudu ne ke bukatar agaji a Syria, yayinda kuma wasu dubu arba'in sukan bar gidajen su tun bayan fara rikicin.