Mandela: Rayuwarsa da iyalansa

Mandela: Rayuwarsa da iyalansa
Image caption Mandela ya yi aurensa na farko ne a shekarar 1944.

Nasarar da ya samu wajen kawar da mulkin wariya da samar da zaman lafiya a duniya, da kuma siyasa ta shafi alakarsa da iyalansa.

Mandela ya auri matarsa ta farko Evelyn a shekarar 1944.

Sun haifi 'ya'ya hudu tare, amma auren ya samu matsala saboda fafutukar Mandela ta siyasa.

A wani lokaci ta yi barazanar kwara masa ruwan zafi idan ya ci gaba da cutar da ita a alakarsu ta aure.

Mr Mandela ya soki yadda Evelyn ke maida hankali kan al'amuran addini. Auren ya mutu a 1950.

Winnie Mandela

A daidai lokacin da mijinta ke ci gaba da zama a gidan yari, Winnie Mandela ta ci gaba da fafutukar ganin an sako shi.

Kuma hakan ya jefa ta cikin tsaka mai wuya inda aka daure ta amma bata ja da baya ba.

An yi mata shari'a a watan Febreru na 1991 kan zargin hannu a kisan wani yaro dan makaranta Stompie Seipei Moeketsi.

Mr Mandela ya marawa matar tasa baya, sai dai jim kadan bayan an wanke ta daga zargin, sai auren na su ya mutu.

Mandela ya kara yin aure karo na uku a 1998 lokacin yana dan shekara 80.

A wannan karon ya auri Gra├ža Machel, tsohuwar matar Samora Machel, tsohon shugaban kasar Mozambique.

Wanda ya mutu a 1986 a wani hadarin jirgin sama da ake zargin shugabannin wariyar launin fata na Afrika ta Kudu da kimtsa wa.

Image caption Tsatson Nelson Mandela