Asusun Unicef ya shirya wa yan jarida taro a Nijar

Tambarin asusun Unicef
Image caption Tambarin asusun Unicef

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya - UNICEF, ya shirya wani taron kara wa juna sani ga yan

jarida a Jamhuriyar Nijar.

Babban makasudin taron dai shi ne kara wa manema labaran sani ta hanyar ba su wasu bayanai da suka shafi hakkin yara musamman 'yan gudun

hijira ta yadda za su yi aikinsu na yada labaran a cikin ka’idojin da suka dace.

A yanzu haka dai dubban yan kasar Mali ne ke zaman gudun hijira a kasar ta Nijar sakamakon yakin da ya barke a can farkon

shekarar da ta gabata.