Ana neman sa wa Koriya ta arewa sabon takunkumi

'Yan kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya
Image caption 'Yan kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya

Amurka ta yi kira a Majalisar dinkin duniya da a sawa Koriya ta Arewa sabbin takunkumi, wadanda a karon farko zasu shafi fannin hada-hadar kudin kasar, akan gwajin makamin nukiliyar da ta yi watan jiya.

Jakadiyar Amurka, a Mjalisar, Susan Rice ta ce Washington na da goyan bayan China na samar da wani daftarin kuduri da za su shafi tura tsabar kudi daga Koriya ta Arewan da kuma abin da ta kira miyagun ayyukan jami'an diplomasiyyar Koriya ta arewan.

Susan Rice ta ce, abin da zan fada shi ne kan kasashen duniya a hade yake akan adawa da shirin makamin nukiliyar Koria ta arewa.

Jakadan kasar China ya ce tilasne a aikewa Koriya ta arewan wata babbar alamar rashin amincewa abin da ta yi.

Tun da farko Koriya ta arewan ta yi gargadin soke yarjejeniyar da ta kawo karshen yakinta da Koria ta Kudu a matsayin wani martani na kakaba mata takunkumi da kuma atisayen sojin da dakarun Amurka keyi da na Koriya ta Kudu.

Karin bayani