'Yan tawaye sun kama sojin majalisar dinkin duniya a Syria

Yaki a Syria
Bayanan hoto,

Yaki a Syria

Mayakan 'yan tawaye a Syria sun kame dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya kimanin 20 a tuddan Golan.

Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya yi kira ga mutanen da su sake su ba tare da wata-wata ba.

Tuni kuma aka tura wata tawagar majalisar dinkin duniyar dake yankin don neman a sako su.

Wani faifan bidiyo da aka sa a internet ya nuna mutane da dama da ke ikirarin 'yan tawayen Syria ne tsaye a kusa da motoci masu silke da aka rubuta sunan majalisar dinkin duniya a jikinsu da dakarun wanzar da zaman lafiyan a ciki.

A waje daya kuma, Kungiyar kasashen Larabawa ta mika kujerar kasar ta Syria a kungiyar ga 'yan tawayen da kasashen yamma ke goyan baya.

Har ila yau kungiyar ta bayyan cewa kasashe mambobinta na iya ba 'yan tawayen Syrian tallin soji.

Yanzu haka kuma sakataren harkokin wajan Birtaniya, Wiiliam Hague ya ce Birtaniya za ta tura wa 'yan tawayen motoci masu sulke da riguna masu sulken, dama wasu kayayyakin yakin, da kuma ba su horo.

Tun da farko, kwamandan kungiyar 'yan tawaye ta Free Syrian Army, Janar Salin Idriss ya yi kira ga kasashen turai da su dage takunkumin kai makamai Syria da suka kakaba wa kasar.