Apple ya bada kai bori ya hau

Apple
Image caption Apple na sahun gaba a kamfanonin latironi na duniya

Kamfanin lataroni na Apple ya bada kai bori ya hau ga iyayen da suka zarge shi da sanya 'ya'ayansu kashe kudi.

A shekarar 2011 ne wasu iyayen da 'ya'yansu suka kashe kudi a kan manhajojin iTunes, wadanda ya kamata ace kyauta ne, suka shigar da kamfanin kara.

Yara dai na kashe fiye da dalar Amurka dari uku kan sayen manhajojin.

Kuma a yanzu Apple na bada kyauta ga iyayen da suka ce 'ya'yansu sun kashe kudi wajen sayen manhajojin ba da saninsu ba, ko kuma su mayar musu da kudaden.

Karin bayani