'An kashe wani jagoran Al-Qa'ida a Mali'

Mali
Image caption Har yanzu ana gwabza fada a wasu sassan Mali

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya ce sojojinsa a arewacin kasar Mali sun kashe daya daga cikin manyan kwamandojin Al-Qaida a arewacin Afrika AQMI, Abdulhamid Abou Zeid.

A ranar Alhamis tashar Talabijin din Algeria ta rawaito cewa an kashe Abou Zeid amma ba'a tabbatar da hakan ba ta wata majiya daban mai zaman kan ta.

Jami'an tsaron Algeria suna gudanar da binciken kwayoyin hallita daga wasu 'yan uwan Abou Zeid su biyu bayan labarin kashe shi a kusa da kan iyaka da Algeria.

Sojojin Faransa tare da taimakon sojojin Chadi da na Mali suna kokarin kakkabe mayakan Ansaruldeen da na Abzinawa wadanda suka kwace arewacin Mali a bara.