Muhimman bayanai kan zaben Kenya

'Yan kasar Kenya za su fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa da 'yan majalisu ranar 4 ga watan Maris a daidai lokacin da suke tunawa da tashin hankalin da ya biyo bayan zaben 2007. Shugaba Mwai Kibaki ba ya neman tazarce - abokin shugabancinsa a gwamnatin hadin gwiwa, Fira minista Raila Odinga, na sahun gaba a zaben shugaban kasa.

Kabilanci

Kenya ta shirya domin zaben kasa baki daya, tare da fargabar cewa za a iya maimaita mummunan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2007. Jama'ar kasar miliyan 42 sun rabu kusan gida 40 ta fuskar kabilu daban-daban, kuma mafiya yawansu na la'akari da wannan wurin zabe. Wasu jama'ar sun dade suna fama da sabani da juna kan batun mallakar filayen noma, da samun ruwa ga dabbobi, wanda a wasu lokutan ke haifar da tashin hankali.

Zaben shekara ta 2007

Da dama daga cikin 'yan siyasa na ganin hanyar samun nasarar zabe na da alaka da kulla kawance da kabilu. A shekara ta 2007, jami'iyyar ODM ta Raila Odinga ta samu goyon bayan kabilarsa ta Luo, da makwaftanta na Luhya, Kalenjins da sauransu. 'Yan kabilar da ta fi kowacce girma ta Kikuyu, sun goyi bayan dan takarar shugabancin kasar da ya fito daga cikinsu Mwai Kibaki, yayin da ODM ta samu goyon bayan kabilar Kamba a Kudanci da Gabashin Nairobi.

Tashin hankali

Bayan zaben, Odinga ya ce magoya bayan Kibaki sun tafka magudi sannan suka fara zanga-zanga a kan tituna. Nan take zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali, sannan aka koma hare-hare tsakanin kabilu musamman a yankin Rift Valley, inda Kikuyu da Kalenjin ke fadi-tashin mallakar filaye. An kona 'yan kabilar Kikuyu talatin da biyar a wata coci a Eldoret. An kuma samu mummunan tashin hankali a Naivasha da Nakura.

'Yan gudun hijira

Kimanin mutane 1,000 ne aka kashe yayin da wasu 600,000 suka bar gidajensu. Shekaru biyar bayan haka, kusan mutane 100,000 na zaune a sansanonin 'yan gudun hijira. Ganin cewa har yanzu akwai tunanin abinda ya faru a zukatan mutane, wasu na fargabar zaben na 4 ga watan Maris zai iya haifar da sabon tashin hankali.

Kawancen siyasa

Akwai 'yan kasar Kenya hudu da ke jiran shari'a a kotun hukunta laifukan yaki ta duniya a watan Afrilu. Daya daga cikinsu - Uhuru Kenyatta - dan takarar shugaban kasa ne, yayin da daya kuma - William Ruto - shi ne abokin takararsa. Sai dai duka an zarge su da tunzura magoya bayansu su kaiwa juna hari. Mr Kenyatta, wanda dan kabilar Kikuyu ne, ya goyi bayan shugaba Kibaki, yayin da Mr Ruto, dan kabilar Kalenji, ya goyi bayan Mr Odinga. Duka mutanen biyu sun musanta zargin.

Karin bayani