Guinea: anyi tashin hankali a Conakry

Image caption Tashin hankalin da aka taɓa yi a Guinea

Ma'aikatan kiwon lafiya a Guinea sun ce, an kashe mutum guda, wasu da dama kuma sun jikkata yayin da jami'an tsaro suka budewa wasu mutane wuta a yankin Koloma na Conakry, babban birnin kasar.

Wannan lamari dai ya biyo bayan kwanaki ne da aka kwashe ana tashin hankali a birnin tsakanin masu goyon bayan bangaren adawa da kuma jami'an tsaro, da kuma wadanda basa ga maciji da juna daga kabilu daban-daban.

Su dai 'yan adawar kasar suna nuna rashin nuna rashin amincewa ne da zaben da ake shirin yi cikin watan Mayu, suna zargin cewa, gwamnati ta shirya murde zaben.