Kenya: an kammala yaƙin neman zaɓe

'Yan takara a Kenya
Image caption Kenya na shirin zabe a ranar Litinin

A ranar Asabar ne 'yan takarar shugabancin kasar Kenya suka yi gangamin yakin neman zabe na karshe, gabanin zaben kasa baki daya da za'a yi a Kenya ranar Litinin mai zuwa.

Na gaba gaba a takarar shugabancin kasar wato, Raila Odinga da Uhuru Kenyatta sun yi jawabai ga magoya bayansu a birnin Nairobi, inda suka yi kiran a zauna lafiya da juna

'Yan takara biyu dake kan gaba, wato Raila Odinga da Uhuru Kenyatta 'ya 'ya ne ga abokan gabar siyasa da su ka yi zamaninsu kusan shekaru hamsin da su ka gabata.

Tashin hankali dai ya biyo bayan zaben shugaban kasar Kenyan da aka yi shekaru biyar da su ka gabata, inda aka kashe mutane fiye da dubu.

Karin bayani