Ba mu tsagaita bude wuta ba - Shekau

Abubakar Shekau
Image caption An dade ana rade-radin batun sulhu tsakanin gwamnati da kungiyar

Kungiyar Jama'atu Ahlil Sunnah Lid da'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram, ta ce ba za ta yi sulhu da gwamnatin Najeriya ba, a cewar shugaban kungiyar Abubakar Shekau.

A wani sakon bidiyo na tsawon minti tara da aka rabawa manema labarai, Imam Abubakar Shekau ya musanta rahotannin da ake bayarwa na cewa ta dakatar da bude wuta kuma sun yi sulhu tare da hukumomin Najeriya.

"Ba mu taba yin sulhu ba, kuma babu yadda za mu yi sulhu da gwamnati a halin da ake ciki," a cewar Shekau.

A baya an ruwaito wani mai suna Imam Abdulazeez a wani taron manema labarai a birnin Maiduguri na jihar Borno, yana cewa yana wakiltar shugaban kungiyar Imam Shekau ne, inda ya ayyana sulhu tsakanin kungiyar ta Boko Haram da gwamnati tare da dakatar da kai hare-hare.

'Ba abu ne mai yiwuwa ba'

Wannan dai shi ne sako na farko da shugaban na kungiyar Boko Haram ya fitar cikin lokaci mai tsawon gaske.

Shugaban na Boko Haram yace kwata-kwata bai san wani mutum mai suna Abdulazeez ba, wanda yayi ikirarin magana da yawun kungiyar, bare ma a yi batun cewa ya wakilce shi a taron manema labarai.

Abubakar Shekau ya nanata cewa batun sulhu da gwamnati a yanzu ba abu ne mai yiwuwa ba, saboda abin da ya kira kama 'yan-kungiyarsu ba dare ba rana da hukumomin Najeriya ke yi.

"Akwai ka'idojin sulhu da addinin Islama ya shimfida kuma wadannan ka'idodjin ne muke bi, amma yadda ake kama 'yan uwa ciki har da mata da kananan yara, alama ce ta cewa hukumomin Najeriya ba da gaske suke yi ba game da sulhu".

Jawabin na Abubakar Shekau dai bai kunshi batun wasu iyalan kasar Faransa su bakwai ba da aka sace a kasar Kamaru wadanda wani mutum da yayi ikirarin cewa shi dan kungiyar ne, ya ce su suka sace su ba.

Karin bayani