An kashe 'yan Boko Haram 20 a Borno

Sojin Najeriya
Image caption An yi artabu a garin Munguno na jahar Borno

Rundunar hadin gwiwar sojan Najeriya dake aiki a jihar Borno ta ce, yau da asubahi ta kashe mayaka ashirin na kungiyar nan da ake kira Boko Haram, a garin Monguno.

Kakakin rundunar yace, an kashe 'yan kungiyar ta Boko Haram ne yayin da su ke kokarin kai hari akan wani barikin soja dake garin na Monguno.

Rundunar hadin gwiwar sojojin ta kuma ce ta samu nasarar samo makamai da su ka hada da bindigogi daga maharan.

Wannan lamari dai na zuwa ne kwana guda bayan da Shugaban Kungiyar Boko Haram Imam Abubakar Shekau ya musanta cewa kungiyar ta dakatar da bude wuta kuma tayi sulhu tare da hukumomin Nijeriya.

Karin bayani