Congo: Mutane 30 sun mutu a hadarin jirgi

Congo
Image caption Hatsarin jirgi ya yi sanadiyyar rayuka a Congo

Jami'ai a jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun ce wani jirgin sama ya fadi a birnin Goma a gabashin kasar, inda mutane talatin suka mutu.

Jirgin, wanda ya taso daga garin Lodja dake yankin tsakiyar kasar, mallakar wani kamfanin kasar ne mai suna CAA.

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo dai ta kasance daya daga cikin kasashen da basu da ingantacciyar hanyar sufuri ta sama a duniya.

Karin bayani