Kasuwar kekuna na bunkasa a Kano

Kasuwar kekuna na bunkasa a Kano
Image caption Jama'a da dama ciki harda mata sun koma hawa keke a Kano

Jama'a da dama a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun koma hawa keke tun bayan da gwamnatin jihar ta hana goyo a kan babur.

Wanann dai ya sa masu sana'ar sayar da kekuna kara samun tagomashi, inda kuma farashin kekunan ya karu matuka gaya.

Wakilin BBC a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai, ya ce a baya dai jama'a da dama musamman 'yan birni na daukar hawa keke a matsayin koma baya ko kaskanci ko rashin wayewa.

Sai dai a yanzu da yake jama'a sun ga uwar bari, hawa keken ya fara zama wata burgewa tun bayan matakin gwamnati na hana daukar mutane a bubura.

'Har da mata ma....'

Abubakar Saminu Dandago, wani mai hawa keke a Kanon cewa yayi: "Na gano cewa keke yafi komai, inda za ka je a minti 15 a babur, yanzu minti uku za ka yi a keke".

Idan zan tafi makaranta ina bata lokaci a titi, ga shi kuma an hana hawa babur, keke ya fi komai sauki, a cewar wani dalibi da ya je sayen keke.

Na samu sauki sosai saboda yanzu na daina kashe kudin mota tun da na fara hawan keke.

"Harkar kasuwa ta bunkasa, saboda masu hawa keke sun karu....kuma manya ne ke sayen kekunan ba wai yara ba, a cewar Nura sabi'iu Abdullahi shugaban masu sayar da kekuna a Kano.

"Har ta mata ma suna hawa kekunan...za ka gansu a kan tituna suna tafiya makaranta", kamar yadda ya ce.

Yayin da masu sana'ar keke ke murnar budewar kasuwa, su kuwa masu sana'ar achaba kokawa suke yi saboda matakin gwamnati na kafa dokar hana daukar mutane a kan babur a wasu yankunan birnin wacce tuni gwamna ya sanya wa hannu.

"Yan achaba da dama sun yi yaushi, sun bushe saboda rashin aikin yi....da dama daga cikinmu mun fara sakin matanmu, " a cewar Muhammad Sani Hassan shugaban 'yan achaba na Najeriya.

Ya yi kira ga gwamnati da ta hanzarta wurin cika alkawuran da ta yi musu domin kawar da radadin hana su gudanar da sana'ar ta su.

A yanzu haka dai masu babura a birnin na yin rijistar ababan hawansu, kuma gwamnatin ta ce kawo yanzu komai na tafiya daidai ba tare da wata gagarumar matsala ba.

Ko da dai dole ce ta sa jama'a durfafar kekuna yanzu, masana harkar lafiya na cewa hawa keken da jama'a suke yi zai taimaka musu wajen samun ingantacciyar lafiya, tun da dai tukin keken motsa jiki ne wanda ke da muhimmanci ga lafiyar jama'a.

Karin bayani