Ana zabe a kasar Kenya

Image caption Tun da karfe shida ne agogon Kenya, mutane da dama suka fito domin kada kuri'a

Al'ummar kasar Kenya na babban zabe, abin da masana ke kallo a matsayin zabe mafi mahimmanci a tarihin kasar.

Wannan ne karo na farko da ake zabe a kasar, tun bayan da aka yi garanbawul ga kundin tsarin mulkin kasar domin kaucewa irin tashin hankalin da ya auku a kasar bayan zaben da aka gudanar a shekarar ta 2007.

Sama da mutane 1,000 ne da ba basa ga maciji da juna suka rasa rayukansu, bayan rikicin da ya barke a wancan lokacin.

Duk da cewa dai an yi ganganmi neman zaman lafiya, rahotanni sun ce an kashe jami'an 'yan sanda biyu a kusa da Mombasa da safiyar ranar Litinin.

Jami'ai sun ce wasu gungun mutane ne suka kaiwa 'yan sandan hari, a yankin Changamwe a bayan garin Mombasa.

Al'ummar Kenya za su zabi, 'yan majalisa da gwamnonin lardi da kuma yan majalisun lardi.

Sai dai duniya ta sanyan ido ne a kan zaben shugaban kasa.

'Yan takara takwas ne ke neman kujerar shugaban kasa, amma yan takarar dake gaba-gaba sune fira minista mai ci a yanzu, Raila Odinga da kuma Uhuru Kenyatta.