An bude majalisar dokokin Nijar

Hama Hamadou
Image caption Hama Hamadou ya yi takarar neman shugabancin jamhuriyyar Nijar

A jamhuriyar Nijar, majalisar dokokin kasar ta soma zaman taronta na farko na shekarar 2013, inda za su tattauna a kan ayoyin doka da dama.

A tsawon wannan lokacin ne kuma majalisar za ta gayyato jami'an gwamnati, domin su bada bahasi game da wasu batutuwan da 'yan majalisar ke son karin haske a kai.

Sai dai shugaban majalisar, malam Hama Amadu ya yi amfani da damar ta bude majalisa, wajen musanta labarin da ke cewa babu cikakken shiri tsakaninsa da shugaban kasa, Alhaji Mahamadu Issoufou.

Lamarin da ke barazana ga zaman kawancen na MRN mai mulki a kasar ta Nijar.

Jam'iyyun PNDS ta Mahamadou Issoufou da Moden Lumana ta Hama Amadu ne dai manya-manyan ginshikai a kawancen.

Dan majalisar na jam'iyyar adawa ta MNSD Nasara, Dauda Jigo yace suna zura ido game da cece-kucen dake tsakanin jam'iyyun kawancen dake mulkin kasar.