An sallami Sarauniya Elizabeth daga asibiti

Sarauniya Elizabeth ta Ingila
Image caption Sarauniya Elizabeth ta Ingila lokacin da take barin asibit

Sarauniya Elizabeth ta Ingila ta bar asibiti bayan da aka kwantar da ita saboda ciwon ciki da ke haddasa amai da gudawa, da kuma kullewar ciki.

Sarauniyar ta bar asibitin na tsakiyar birnin London ne bayan shafe kwanaki biyu likitoci suna duba lafiyarta.

Tun ranar Lahadi ne aka kwantar da ita a asibitin King Edward VII - wannan shi ne karo na farko da ta kwanta a asibiti cikin shekaru 10.

An dage wasu ayyuka da aka tsara za ta yi ciki har da ziyara zuwa birnin Rome na kasar Italiya.

Wakiliyar BBC Daniela Relph, ta ce sarauniya Elizabeth, mai shekaru 86, na cikin "koshin lafiya" lokacin da ta bar asibitin.