Senegal za ta rufe makarantun allo

Senegal za ta rufe makarantun allo
Image caption Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun sha yin gargadi game yanayin wasu makarantun allon

Shugaban kasar Senegal, Macky Sall ya ce gwamnatinsa za ta rufe duk makarantun allon da ba su cimma matakan kare lafiyar da suka kamata ba.

Kalaman na sa dai sun zo ne bayan wasu yara tara sun mutu a wata gobarar da ta tashi a wata makarantar allo da ke kusa da babban birnin kasar, Dakar.

Gobarar dai ta tashi ne, a yayin da yara 45 masu shekaru shida zuwa 12 ke barci a daki daya, wanda aka gina da katako kuma aka yi masa rufin kwano a gundumar Medina.

Ana dai tunanin wutar kendir ce ta haddasa gobarar a ranar Lahadin da ta gabata.

Kuma a lokacin da ya kai ziyara inda gobarar ta auku ne, Mr. Sall wanda Musulmi ne, yace daga yanzu duk makarantar allon da ke ci da gumin yara, kuma ba ta tabbatar da kare lafiyarsu to za a rufe ta.

Sannan za a maida yaran gurin iyayensu.

Muhalli mara kyau

Wakilin BBC a Dakar Thomas Fessy yace, kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun sha yin gargadi game da wurare marasa kyau da ake ajiye yara a karkashin ilimin tsangaya.

Haka kuma akwai zargin da ake wa wasu malaman makarantar allon da ci da gumin almajirai.

Yawancin yaran da ake kaiwa karatun na tsangaya na kare wa a matsayin almajirai, inda suke yawon bara, suna neman kudi da abinci domin su kaiwa malaman.

Motocin kashe gobara sunyi ta fama kafin su shiga lungun da makarantar take, abin da ya kawo jinkiri wajen kashe gobarar.

Magajin garin Dakar, Khalifa Sall ya bayyana wa wani gidan radiyon kasar cewa, muhalli mara kyau dake cunkoson jama'a da ake da su a wannan sashen na birnin ne yasa masu kashe gobara suka kasa kutsawa domin yin aikinsu kamar yadda ya kamata.