'Ya kamata a yi wa Boko Haram afuwa'

Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Abubakar Sa'ad na uku
Bayanan hoto,

Mai yiwuwa gwamnatin Najeriya ta saurari kiran da Sarkin ya yi

Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Abubakar Sa'ad na uku, ya yi kiran da a baiwa 'yan kungiyar Jama'atu Ahlil Sunnah Lid da'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram afuwa.

Ya bayyana cewa wannan matakin zai taimaka wurin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake fama da su a arewacin kasar.

"Za ta sa matasa da dama su fito daga wurin buyansu domin rungumar shirin, kuma koda mutum daya ne ya fito fili sai a rungume shi domin isa ga sauran."

Kungiyar Boko Haram da sauran 'yan bindiga na tayar da kayar baya a sassan arewacin kasar da dama, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan jami'an tsaro da fararen hula.

Abaya dai an yi kokarin tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar ta Boko Haram, lamarin da ya ci tura. A makon da ya gabata ma kungiyar ta karyata rahotannin da ke cewa ta tsagaita wuta.

Jagoran al'ummar musulmi

Sarkin wanda ke magana a wurin wani babban taro na kungiyar Jama'atul Nasrul Islam a Kaduna, ya bayyana matsalar tsaro a matsayin wata babbar matsala da ya kamata gwamnati ta warware.

Jama'a da dama sun sha yin kiran gwamnati da ta yi musu afuwa domin fara tattaunawa da su, amma hakan bai yiwu ba.

Sai dai Editan sashin Hausa na BBC Mansur Liman, ya ce akwai yiwuwar gwamnatin Najeriya ta duba kalaman Sarkin, kasancewarsa jagoran al'ummar musulmi a kasar.

Taron ya kunshi malaman addinin Islama da kuma Sarakunan gargajiya Musulmai na kasar.

Shugabannin za su mayar da hankali ne bisa matsalolin tsaro da kiwon lafiya da kuma tattalin arzikin da suka addabi kasar musamman ma a arewacinta.