Buhari ya soki tsarin zabe a Najeriya

Image caption Janar Muhammadu Buhari

Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta CPC a zaben shekara ta 2011, Janar Muhammadu Buhari ya ce, har yanzu ba a je ko'ina ba dangane da gyara ga tsarin zaben Najeriya.

Yayin wata lacca da ya gabatar a taron da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje suka shirya da hadin gwiwar 'yar majalisar dokokin Birtaniya, Diane Abott, Buhari ya kuma ce, matsalar Najeriya ita ce, cin hanci da rashawa da kuma lalacewar sha'anin mulki.

Janar Buhari ya ce yanzu babban karan tsaye shine shirya zabe cikin gaskiya da adalci.

Ya ce ko da an murde zabe anje kotu, an gudu ne kawai ba'a tsira ba.

"Ya kamata a Hukumar zabe ta Najeriya ta tabbatar an gudanar da zabe a kan adalci kuma bisa ka'ida." in ji Buhari.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce sake fasalta Najeriya ba zai kawo karshen matsalolin da ake fuskanta ba a kasar.

Janar Buhari ya ce shugabanci na gari ne kawai zai iya sanya kasar kan turbar ci gaba.

Laccar da aka yi a majalisar dokokin Birtaniya ta samu halartar 'yan Najeriya da dama dake zaune a Birtaniya.