Shugaban Venezuela Hugo Chavez ya rasu

Shugab Hugo Chavez
Image caption Marigayi Hugo Chavez ya rasu ne yana shekara 58 a duniya

Mataimakin shugaban kasar Venezuela ya bayyana rasuwar shugaban kasar Hugo Chavez bayan ya yi fama da wata doguwar rashin lafiya.

Mr Chavez dai bai fito a bainar jama'a ba tun bayan da ya dawo daga Cuba inda aka yi mishin maganin ciwon sankara.

Mataimakin shugaban kasar Nicolas Maduro ya bayyana rasuwar shugaban kasar ne cikin kaduwa.

Shugaban kasar mai shekarun haihuwa 58 ya yi fama da matsalar nunfashi ne kafin ya rasu.

Ministan kula da harkokin kasashen waje Elias Jose Jaua Milano ya bada sanarwa hutu kwanaki bakwai domin jimamin shugaban kasar, sannan ya ce za'a yi jana'izar sa ne a ranar Juma'a.

Ministan ya ce mataimakin shugaban kasa Nicolas Maduro zai jagoranci kasar kafin a gudanarda da zabe nan da kwanaki 30.

Sakonnin ta'aziyya

Shugaba Obama wanda suka samu sa'insa da Hugo Chavez a lokacin da yake raye ya ce Venezuela na fuskantar kalubale sakamakon mutuwar shugaban nata, sanna ya ce kasar Amurka na sake jaddada cewa shirye take da ta ci gaba da taimakawa al'ummar kasar.

Shima jakadan Rasha a majalisar dinkin duniya cewa ya yi;

"abin tashin hankali ne, Mr Chavez wani gwarzon dan siyasa ne ga kasarsa,da yankin latin amurka kai harma da duniya baki daya daya."

Shugabar kasar Argentine Cristian Fernandes ta ce ta soke duk wasu abubuwa da za ta yi a lokacin da ta samu labarin rasuwar abokinta kuma ta ayyana kwanaki uku da za a yi jimami a kasarta.

Shima Tsohon Shugaban kasar Cuba Fidel Castro ya yi jimamin rasuwar mutumin da yake tamkar da a gare shi kuma kasar Cuba ta ce ranar da za a yi jana'izar Chavez rana ce ta hutu ga al'ummar kasar.

Karin bayani