Wen Jiabao ya yi jawabin karshe

Image caption Wen Jiabao

Primiyan China mai barin gado, Wen Jiabao ya yi jawabinsa na karshe a siyasance.

A jawabin da ya yi game da aikin da gwamnatin take shirin yi, Primiyan ya yaba da irin nasarorin da gwamnatin kasar ta samu cikin shekar biyar da su ka wuce a yayinda kuma ya bayyana irin shirin da gwamnatin ta tsara a shekara ta 2013.

Masu adawa da gwamnatin China ta yanar gizo dai sun soki jawabin na Premier.

A wani jawabi da ya yi mai tsawon gaske, Premiern China mai barin gado Wen Jiaboa ya jinjinawa jami'an kasar saboda irin nasarorin da aka samu a kasar a cikin shekaru biyar da su ka gabata.

Wen ya bayyana irin nasarar da kasar ta samu wajen tunkarar matsalar tattalin arziki da ke fuskanci duniya.

Ya dai bayyana irin tsare-tsare da gwamnati za ta aiwatar a shekara ta 2013, inda yace sabuwar gwamnati mai shigowa za ta maida hankali ne wajen inganta rayuwar alummar kasar.

Ya kuma ce za'a kara yawan kudaden da aka ware na biyan kudaden fansho da kashi 10.

Sai dai wasu 'yan kasar China da dama a yanar gizo, musamman man ma a shafin Weibo sun soki jawabin na Primiya mai barin gado.

Sun ce bai bada cikakken bayani ba kan yadda gwamnati za ta aiwatarda alkawuran da ta yiwa al'ummar kasar, musamman ma kalubalen da kasar ke fuskanta na gurbacewar muhalli da kuma cin hanci da rashawa a gwamnati.