Duba yadda za'a kare ma'ikatan rigakafi a duniya

Image caption Masu allurar polio na fuskantar hare-hare a kasashe kamar su Najeriya da Pakistan

A yau ne za a fara wani taro na kwanaki biyu tsakanin wasu malaman addinin Musulunci da jami'an hukumar lafiya ta duniya, WHO, a birnin Alkahira na kasar Masar.

Taron zai lalubo hanyoyin kawo karshen hare-haren da ake kaiwa masu digon maganin rigakafin cutar polio a wasu kasashe.

Za a gudanar da taron ne a asirce inda za kuma a tattauna rawar da al'ummar musulmi za su taka dan tabbatar da cewa an kare dukkan yara daga kamuwa da cutukan shan inna mai nakasa yara da kyanda da ma sauran cututtuka.

Kimanin ma'aikatan riga-kafin shan inna 20 ne aka kashe a Pakistan da Najeriya cikin watanni uku da suka gabata

Hakan dai wani babban koma baya ne ga fafutukar kawo karshen cutar polio a duniya.

Kasashen Najeriya da Pakistan da Afganistan ne kawai har yanzu suka rage a duniya suna fama da cutar ta polio.

A arewacin Najeriya musamman, mutane na ci gaba da kyamar allurar rigakafin cutar ta Polio.