Ana jana'izar Hugo Chavez a Venezuela

An fara jana'izar Hugo Chavez
Image caption Shugabannin kasashe da dama ne ke halartar bikin

An fara jana'izar shugaban Venezuela Hugo Chavez a Caracas babban birnin kasar.

Kimanin shugabannin kasashen duniya 30 ne ke halartar bikin a makarantar sojoji inda dandazon jama'a suka taru a waje.

Nan gaba, za a rantsar da mataimakin shugaban kasa Nicolas Maduro a matsayin shugaban riko. Wajibi ne ya sanya ranar gudanar da zabe cikin kwaniki 30.

Hugo Chavez, wanda ya shugabanci Venezuela tsawon shekaru 14, ya mutu ranar Talata yana da shekaru 58 bayan da ya dade yana fama da cutar daji.

Mataimakin shugaban kasa Maduro ne ya fara bude bikin da sanya takobi kan gawar Mr Chavez - takobin na Simon Bolivar ne - wanda ya jagoranci neman 'yancin kan kasar a karni na 19.

Daga nan ne shugabanni suka fara yin layi domin girmamawa ga gawar ta sa.

Rukunin farko shi ne na shugabannin Latin Amurka - wadanda suka kunshi Raul Castro na Cuba, Sebastian Pinera na Chile da Rafael Correa na Ecuador.

Wani rukunin kuma shi ne na kawayen Mr Chavez daga wajen yankin, shugaban Iran President Mahmoud Ahmadinejad da Alexander Lukashenko na Belarus.

An kuma karanto sakon shugaban kasar Syria Bashar al-Assad.

Karin bayani