Kenyata na kalubalantar hukumar zaben Kenya

Kenyatta
Image caption Sakamakon farko ya nuna cewa Mr Kenyatta ne a kan gaba

Wata takaddama ta barke a Kenya a kan ko a sa kuri'un zaben shugaban kasar da suka lalace a cikin wadanda za'a kirga.

Gammayar jam'iyyun da Uhuru Kenyata ke jagoranta sun ce bai kamata a sa lalatattun kuri'un ba, abin da zai taimaka ya yi nasara a zagayen farko na zaben.

Masu aiko da rahotanni sun ce 'yan kasar Kenya na kara kosawa game da jinkirin bayyana sakamakon zaben, suna fargabar sake afkuwar rikicin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2007.

Sakamakon da aka fitar kawo yanzu dai na nuna cewa Mr Kenyatta na gaban babban abokin hamayyarsa, Raila Odinga.

Karin bayani