'Yan gudun hijiran Syria sun kai miliyan daya

Wasu yara 'yan Syria a sansanin 'yan gudun hijira
Image caption Kasar Lebanon kadai ta tsugunar da kashi talatin cikin dari na 'yan gudun hijirar Syria

Majalisar dinkin duniya ta ce yawan mutanen da suka tsere wa rikicin Syria sun kai miliyan daya.

Kwamishina mai sa ido kan harkar 'yan gudun hijira na majalisar ya ce, yawan mutanen dake ketara wa kasashen dake makotaka da Syria, domin neman mafaka ya karu tun a farkon wannan shekarar.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya rabin 'yan gudun hijiran dai yara ne, kuma shekarunsu sun kama daga kasa da shekaru 11, yawancinsu na cikin kaduwa game da halin da suka tsinci kansu.

Mafi yawa daga 'yan gudun hijiran dai suna zaune ne a kasashen Jordan da Lebanon da Turkiyya da Iraq da kuma Masar.

"Syria na dumfarar fadawa cikin bala'i, " A cewar kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres,kuma ya yi gargadin cewa kayayyakin agajin da ake kaiwa na karanci.

"Dole a dakatar da wannan lamari," yana mai cewa yawan mutanen dake tudadowa daga Syria, na kokarin fin karfin kasashen dake makotanta da ita.