An fara bikin jana'izar Hugo Chavez

An fara bikin jana'izar Shugaban kasar Venezuela, Hugo Chavez a yayinda aka ajiye gawarsa a wata cibiyar soji dake birnin Caracas domin girmama shi.

Mahaifiyarsa da 'yayansa sun zagaye akwatin gawar mamacin domin yi mishi addu'o'i.

Shugabannin kasashen Argentina da Bolivia da kuma Uruguay sun halarci bikin girmama gawar.

Manya jami'an gwamnati da na soji ne suka fara girmama gawar kafin a bari sauran al'ummar kasar su fara shigowa.

Bikin jana'izar da aka fara na girmama gawar Mista Chavez ya sosa rai sosai a yayinda aka dauko gawar ta so daga asibitin sojin da ya rasu zuwa wata cibiyar sojin kasar, inda nan ne ya fara horo kafin ya shiga aikin soji.

Girmamawa

Dubun dubatar magoya bayan Chavez ne su ka fito kan hanya domin girmama gawar Marigayin a yayinda suke sanya jan kaya.

An dai lullube akwatin gawar ne da tutar kasar.

Magoya bayansa da dama ne suka rika sharara kuka a yayinda suke ta kokarin taba akwatin gawar domin nuna kaunar da suke masa.

A cibiyar sojin kasar inda aka ajiye gawar domin girmamata.

Shugabannin kasashen Argentina da Urugauy da kuma Bolivia na cikin wadanda su ka halarci bikin girmama gawar a yayinda aka shirin binne shi a ranar juma'a.

Makomar kasar

A yanzu dai hankali ya karkata ne kan makomar kasar. Kudin tsarin mulkin kasar dai ya yi nuni da cewa idan an samu gibi a mukamin kujerar shugaban kasa kamar yadda ta faru a yanzu, toh kamata ya yi a a shirya zaben cikin kwanaki 30.

Gwamnatin kasar dai ta ce za ta dokar. Kafin marigayi Chavez ya tafi neman magani a kasar Cuba a shekarar da ta gabata, ya nada mataimakinsa a matsayin wanda zai gaje shi.

Har yanzu dai 'yan adawar kasar kasar basu maida martani ba gama da makomar kasar, amma majiyoyi da dama na nuni da cewa wanda ya yi takara a Hugu Chavez ne a watan Okutoban baran Henrique Capriles Rodonsky zai sake tsayawa takara.