'An yi almudahana a zaben Kenya'

Kidayar kuri'u a Kenya
Image caption Wannan ne karon farko da Kenya ta fara bin tsarin amfani da na'uri a zabe

Dan takarar mataimakin shugaban kasa ga firai minista Raila Odinga, ya ce akwai hujjojin dake nuna cewa an yi almudahana a sakamakon zaben shugaban kasa a Kenya.

Inda ya nemi da a dakatar da kidayar kuri'un.

Sai dai Kalonzo Musyoka yace ba ya kiran mutane su fito domin su yi bore a kan tituna.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Nairobi.

Ya ce "An samu matsala da na'urar da ake kidaya kuri'un, muna da shaidar da ke nuni da cewa, akwai aringizo a sakamakon zaben."

Ya kara da cewa "Za mu iya cewa, adadin kuri'un da aka kada ya zarta yawan masu kada kuri'un da suka yi rijista."

Mr. Musyoka ya ce ba ya neman mutane su fito kan tituna su yi zanga-zanga.

Wakilin BBC a Nairobi ya ce, al'amura sun tsaya cik a wurin da ake kirga kuri'un har fiye da sa'oi biyu, amma daga bisani an cigaba da aiki.

Inda ya bayyana cewa an cigaba da cewa wakilan hukumar zaben kasar sun shiga wani taron sirri tare da jakadun kasashen waje.

Wakilin ya kuma kara da cewa ana zaman dar-dar, tare da fargabar sake afkuwar abin da ya biyo bayan zaben shekarar 2007 na tashin hankali a kasar.

Sai dai mutanen Kenya da dama za su cigaba da nuna kokwanto game da shaidun da Mr. Musyoko ke magana, muddin ba su ga hakan a zahiri ba.