'Nijar na gaba wajen auren mata 'yan ƙasa da shekaru 18'

Image caption Mahamadou Issoufou, shugaban Niger

Wani rahoton hukumar kula da yawan jama'a ta majalisar ɗinkin duniya ya ce, jamhuriyar Niger ce kan gaba cikin ƙasashen da ake yawaita aurar da 'ya'ya matan 'yan kasa da shekaru sha takwas.

Sabon rahoton na hukumar kula da yawan jama'a ta majalisar dinkin duniya ya nuna cewa daga shekara ta 2011 zuwa ta 2020 fiye da yara mata miliyan dari da arba'in ne da shekarunsu ba su kai ba, za a aurar da su.

Sai dai kuma hukomomin jihohin Damagaram da Maradi inda matsalar ta fi kamari sun ce, suna samun nasara a matakan da suka dauka na rage yawan wannan matsalar.

Dgaga cikin kasashen da rahoton na majalisar ɗinkin duniya yace, matsalar tafi yawa sun haɗa Chadi, da Bangladesh da kuma Guinea.