Amurka ta kama Sirikin Bin Laden

Image caption Abu gaith ana zarginsa da makarkashiyar kashe Amurkawa

Amurka ta kama wani mai magana da yawun Osama Bin Ladan ta kuma caaje shi da laifin makarkashiyar kashe Amurkawa.

Sulaiman Abu Ghaith wanda sirikin marigayi jagoran kungiyar al-Qaeda ne an shirya gurfanar da shi ne a gaban wata Kotu dake New York ranar Jumma'a.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun nuna cewar an kamo shi ne a kasar Turkiyya aka tasa keyarsa zuwa Jordan, daga bisani aka dauko shi zuwa Amurka.

Wasu Sanatoci na jam'iyyar Republican da suka hada da Lindsey Graham sun soki lamirin tuhumar ta sa a cikin Amurka.

Yace, "tambaya ta ga gwamnati ne, me yasa aka ki kai wannan mutum Guantanamo bay inda za a tsare shi a matsayin abokin gaba wanda za a tatsi bayanai daga wurin sa."

Karin bayani