Jonathan ya kalubalanci dattawan Borno

Goodluck Jonathan
Image caption Wannan ne karon farko da shugaban ya ziyarci jihohin a cikin shekaru uku na mulkin kasar

A ci gaba da ziyarar da ya ke yi a jihohin Borno da Yobe wadanda su ka fi fama da rikicin da ake yi tare da kungiyar nan ta jama'atu ahlissunnah lid da'awti wal jihad da wasu ke kira Boko Haram, Shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan a yau ya gana da shugabanni da dattawa da kuma 'yan siyasa na Jihar ta Borno.

Wasu dattawan jahar Bornon dai sun bukaci Shugaban ya bada iznin janye sojoji daga jahar, inda su kai zargin cewa sojojin su na gallazawa jama'ar jahar.

To sai dai a martanin da ya mayar Shugaba Goodluck Jonathan ya kalubalanci dattawan Bornon da har sai sun bashi tabbacin cewar ba za a cigaba da samun asarar rayuka ba idan aka janye sojojin, kafin ya amince da wannan bukata ta su.

Shugaban ya ce gwamnati bata jin dadin irin kudaden da take kashewa akan maganar tsaro a yankin, kudaden da Shugaban ya ce za a iya karkatar da su wajen wasu fannoni na ayyukan raya kasa.

Amma ya ce idan har dattawan zasu sanya hannu kan wata yarjejeniya da shi na cewa idan an janye sojojin ba za a ci gaba da samun asarar rayuka ba, ya ce to a shirye yake ya bada iznin janye sojojin

Haka kuma ya sake jaddada cewa babu maganar yin afuwa ga 'yan kungiyar Boko Haram har sai 'yan kungiyar sun fito sun bayyana aniyarsu ta amincewa da hakan.

Karin bayani