Uhuru Kenyatta ka iya nasara zaben Kenya

Image caption Lokacin da Uhuru Kenyatta ya yi zaben da zai iya samun nasara

Sakamakon share-fage a zaben Shugaban kasa na kasar Kenya ya nuna cewar Uhuru Kenyatta ne ya lashe zaben da 'yar rata wadda za ta kauda bukatar zagaye na biyu na zaben.

Alkaluman da hukumar zaben kasar ta bayar sun nuna cewar Mr Kenyattan ya lashe kashi hamsin cikin dari har ma da 'yan dakikoki na kuri'un da aka kada.

To amma hukumar za ta sake tantance alkaluman kafin ta bayar da sanarwa ta karshe nan gaba a yau, Asabar; kwanaki biyar bayan kammala zaben.

Mr Kenyattan dai na fuskantar tuhuma a kotun binciken miyagun laifukka dangane da hatsaniyar da ta biyo bayan zaben da aka yi a kasar cikin shekara ta 2007.

Karin bayani