Kenyatta ya lashe zaɓen shugaban ƙasa

Image caption Uhuru Kenyatta, ya lashe zaben shugaban kasar Kenya

Hukumar zaɓen kasar Kenya ta bayyana Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.

Uhuru Kenyatta ya kaucewa zuwa zaye na biyu ne a zaɓen ta hanyar samun rinjayen kashi hamsin da digo bakwai cikin dari na kuri'un da aka jefa.

Shugaban hukumar zaɓen Kenyan, Issack Hassan yace, hukumar ta gamsu cewa, anyi zaben cikin gaskiya da adalci, duk da targardar na'ura da aka fuskanta.

Hukumar zaɓen ta Kenya ta kuma ce, a zaben da aka kammala kashi tamanin da shida na masu jefa ƙuri'a ne suka fito.

Tun farko dai wani mai bada shawara ga dan takara na biyu a yawan ƙuri'u, Raila Odinga yace, ba zai amince da sakamakon zaɓen ba.

Shi dai wanda ya lashe zaben, Uhuru Kenyatta yana fuskantar tuhuma a gaban kotun duniya dangane da tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2007 a