Uhuru Kenyatta ya lashe zaben Kenya

Uhuru Kenyatta
Image caption Uhuru Kenyatta dan takarar shugaban kasa a Kenya.

Sakamakon wucin gadi na zaben Shugaban kasa na kasar Kenya ya nuna cewar Uhuru Kenyatta ne ya laashe zaben da 'yar raata wadda za ta kauda bukatar zagaye na biyu na zaben.

Alkaluman da hukumar zaben kasar ta bayar sun nuna cewar Mr Kenyattan ya laashe kashi hamsin cikin dari har ma da 'yan dakikoki na kuri'un da aka kaada.

To amma hukumar za ta sake tantance alkaluman kafin ta bayar da sanarwa a hukumance kwanaki biyar bayan kammala zaben.

Mr Kenyattan dai naa fuskantar tuhuma a kotun binciken miyagun laifukka dangane da hatsaniyar da ta biyo bayan zaben da aka yi a kasar cikin shekara ta 2007.