Akwai gyara a hana fatauci a Birtaniya–Masana

Image caption Gwamnatin david Cameron na kare yadda take yaki da fataucin mutane

Kungiyar wasu kwararrun masana a Birtaniya sun ce kokarin da gwamnati ke yi na ganowa da hana safarar mutane yana bukatar gyara a cikin hanzari.

Kwararrun na Centre for Social Justice sun ce babu cikakkiyar fahimtar yadda matsalar ta yadu - kuma yawanci a kan dauki mutanen da aka yi safarar ta su a matsayin wadanda suka aikata miyagun laifuka.

Kwararrun suka ce kamata ya yi gwamnatin Birtaniya ta nada wani Kwamishina mai kula da fannin yaki da bauta, suka kuma ba da shawarar cewa yakamata a janye yawancin ikon da hukumar kula da kan iyakoki take da su.

Gwamnatin dai ta yi watsi da yawancin sukar da aka yi ma ta tana cewar tsarin da ake amfani da shi yanzu yana aiki sosai.

Karin bayani