Najeriya: an kashe 'yan ƙasashen waje

Ƙasashen Burtaniya da Girka da Italiya sun ce sun yi imanin cewa an kashe turawan nan bakwai da aka yi garkuwa dasu a Najeriya, kamar yadda ƙungiyar da ta yi garkuwa dasu ta bada bayyana.

Ƙungiyar masu kaifin kishin Islama ta Ansarul Muslimina fi Biladis Sudan ta sace mutanen bakwai ne a watan da ya gabata, daga wani kamfanin gine gine a jihar Bauchi.

Ƙungiyar tace ta kashe waɗanda ta yi garkuwar dasu da suka hada da dan Burtaniya da dan, da Italiya, da dan Girka, da dan Labanon, saboda yunƙurin da tace dakarun Burtaniya da na Najeriyar suka yi na ƙwato waɗannan mutane.

Amma ƙasar Italiya ta ce hakan ba gaskiya ba ne.