Italiya ta yarda an kashe 'yan Kasashen waje a Najeriya

Wasu da akai garkuwa da su a Najeriya
Image caption Dan Italiya na daga cikin mutanen da akai garkuwa da su.

Ma'aikatar harkokin wajen Italiya ta ce ta yi imanin cewa an kashe 'yan Kasashen wajen nan bakwai da akai garkuwa da su a arewacin Najeriya

Ma'aikatar harkokin wajen tace binciken da ta yi tare da hadin gwiwar wasu Kassahe, ya nuna cewa ikirarin da masu sace mutanen su ka yi na cewar sun hallaka wadanda su kai garkuwa da su, gaskiya ne

Kungiyar nan ta Ansarul Muslimina fi biladis Sudan ce ta bayyana cewa ta kashe wadanda tai garkuwa dasu su bakwai a wani kamfanin gine gine a arewacin Najeriya

Ana tunanin cewar Kungiyar bangare ce ta kungiyar nan da aka fi sa ni da Boko Haram

Karin bayani