Karzai ya zargi ƙungiyar Taliban da Amurka

Hamis Karzai da Barck Obama na Amurka
Image caption Hamid Karzai ya soki Kasar Amurka

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya zargi kungiyar Taliban da kuma Amurka da kokarin tsoratar da mutane domin su yi imanin za a samu karin tashin hankalin a Kasar bayan dakarun Kasashen Turai sun bar Kasar

Hamid Karzai ya ce hare haren kunar bakin wake na baya- bayan nan a birnin Khost da kuma babban birnin Kasar na Kabul da 'yan Taliban su kai ikirarin kaiwa, an kaisu ne da nufin tsawaita kasancewar Amurka da kuma dakarun Kasashen Turai a kasar Afghanistan.

Hamid Karza ya yi wannan ikirari ne a wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin din Kasar

Sai dai Amurka ta musanta wannan zargi da Shugaban Afghanistan din ya yi.

Karin bayani