Kenyatta ya yi kira a mutunta Kenya

Image caption Uhuru Kenyatta na murnar nasarar da ya samu a Kenya

Sabon Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta wanda ke fuskantar tuhuma a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya yi kira ga kasashen duniya su mutunta 'yancin kasar sa.

Lokacin da yake magana jim kadan bayan nasarar da ya samu a zaben, Mr Kenyatta ya ce idan aka yi haka zai bayar da hadin kai ga dukkan hukumomi na kasashen duniya.

An zarge shi da mataimakinsa da aikata laifuka na cin zarafin bil-adama a tashin hankalin da ya biyo bayan babban zaben da aka yi can baya a kasar ta Kenya.

Dan takarar da ya sha kaye a zaben na baya-bayan nan Raila Odinga ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben a Kotu.

Yace, "nan gaba kadan za mu garzaya Kotu don kalubalantar sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta bayar da sanarwa 'yan sa'oin da suka wuce.

Karin bayani