Kotu ta soke tuhumar da take yi wa Francis Muthaura

Francis Muthaura
Image caption Kotu ta rasa shaida akan caje cajen Francis Muthaura

Masu gabatar da kara sun soma ne da wata sanarwa ta janye caje cajen aikata miyagun laifuka akan bani adama da ake yiwa babban maikacin gwamnatin Kenya Francis Muthaura.

Fatou Bensouda tace an shigar da caje cajen zuwa Kotun ta duniya dake Hague da kyakyawar niyya, amma a ci gaba da binciken da suke yi sai suka gano cewa immadai an kashe wasu mahimman shaidu da ake bukata ko kuma sun bace ba a san inda inda su ka shiga ba.

Wannan a cewar babbar mai gabatar da karar ta Kotun dake Hague ya auku ne duk kuwa da tabbacin hadin kan da suka samu daga gwamnatin Kenya,

An dai yi watsi da wannan kara yanzu ala tilas, bayan da wani wanda zai bada shaida mai mahimmanci ya janye hujjar da ya bayar tunda farko.

Karin bayani