Babu shaidar kisan 'yan Setraco -Inji Najeriya

Kanal Sambo Dasuki
Image caption Akwai wasu iyalai, Faransawa da kungiyar Boko Haram ke garkuwa da su a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce ba a tabbatar da ikirarin kisan 'yan kasashen waje bakwai, ma'aikatan Setraco da aka kama a jihar Bauchi ba.

Saboda haka za ta yi iya bakin kokarinta wajen ceto su, da kuma tabbatar da tsaron lafiyarsu.

Ministan harkokin wajen kasar, Abba Moro ne ya bayyana hakan.

Inda ya kara da cewa, abin takaici ne yadda al'amarin ya kai ga haka.

Ya ce "Duk da cewa kasashen da ma'aikatan suka fito sun yi amanna an kashe 'yan kasashensu, babu hujjar dake tabbatar da hakan, kuma muna fatan suna raye."

Kungiyar masu fafutukar Islama ta Ansarul Muslimina fi Biladis Sudan ce, ta kame mutanen a watan jiya, a wurin da suke aikin gine-gine a arewacin Najeriya.

Kuma tuni kasashen Birtaniya da Italiya da Girka su ka ce, sun yi amanna an kashe mutanen bakwai a Najeriya, kamar yadda kungiyar Ansaru ta bayyana a wani faifan bidiyon da ta sanya a shafin intanet.

A cewar kungiyar, ta kashe 'yan kasashen Birtaniya da Italiya da Girka da Lebanon da ta yi garkuwa da su ne, saboda yunkurin da dakarun Birtaniya da na Najeriya suka yi na ceto su.

Amma Italiya ta ce babu kamshin gaskiya a wannan batu.

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, William Hague, ya yi tur da al'amarin.