Cardinals za su fara zaben Paparoma

Malaman Katolika wanda ake kira Cardinals a yanzu haka sun taru a birnin Rome inda idan anjima a yau ne za su zu fara zaben sabon Paparoma.

A makon da ya gabata ne suka hallara a birnin na Rome domin tantance wadanda suke ganin ya kamata a nadawa mukamin na Paparoma, inda suke duba cancantar ko kuma rashin cancantar wanda ya kamata a zaba.

Za'a kada kuri'ar ne cikin sirri.

Za'a fara ne da taron adu'o'i na musamman a mujami'ar St Peters, inda a nan ne Cardinals din za su fara shirin zaben na sabon Paparoma.

Da rana ne kuma za su yi maci zuwa cocin Sistine suna wake-waken ibada, sannan kuma kowanne zai rantse da cewa ba zai bayyana abun da ya gudana ba a lokacin zaben na su.

Daga nan ne kuma za'a bada umarni a harshe latin na cewa kowa ya fita da cocin, sai a bar Cardinals din kawai.

Bayan hakan ne kuma za'a fara kada kuri'a.

Idan dan takara daya cikin wadanda Cardinals din su ka tantance bai samu kuri'un kashi biyu cikin uku ba, za'a a sake zaben.

Haka kuma za ayi ta yi sai an samu wanda yake da kuri'un da su kai kai kashi biyu cikin uku na kuri''un da aka kada, sannan sai a bayyana shi a matsayin Paparoma.

Daya daga cikin wadanda ake gani shine kan gaba na samun kuri'un zama Paparoman shine Cardinal Scola daga Milan.

Daya kuma shine dan kasar Brazil Cardinal Scherer.

Amma jama'a da dama dai sun sace cewa abun ne me muya a yi saci fadi game da zaben na Paparoma.