Al'ummar Falklands sun zabi Burtaniya

Al'ummar tsibirin Falklands sun kada kuri'ar raba gardama inda su ka amince su ci gaba da zama karkashin iko Burtaniya.

Hakan ya biyo takkadamar tsawon shekaru 31 kenan tsakanin Argentina da Burtaniya abun da kuma ya kaisu ga yaki a kan tsibirin.

Kuri'u dubu daya da dari biyar da goma sha bakwai ne aka kada a cikin kwanaki biyu da aka yi ana zaben raba gardama, inda hakan ke nufin cewa kashi ca'sain na al'ummar tsibirin ne suka fito kada kuri'a.

A cikin kuri'un da aka kada, mutane dubu daya da dari biyar da goma sha uku ne su ka amice da a ci gaba da zama karkashin mulkin Burtaniya a yayinda mutane uku kawai ne su ka ce basu yarda ba.

Tuni da gwamnatin Burtaniya ta amince da kuri'ar da aka kada inda kuma ta bukaci kasashen duniya su amince da zaben da al'ummar tsibirin su ka yi.

Al'ummar tsibirin sama da dubu daya ne suke da shaidar zaman yan kasar Burtaniya sannan gabaki daya al'ummar tsibirin basu kai dubu uku ba.

Argentina ta yi watsi da zaben raba gardaman da aka yi inda ta ce ba shi da tasiri inda ta ce Majalisar Dinkin Duniya ce kawai ke da hurumin shiga tsakanin kasashen biyu.

Argentina dai na kiran tsibirin Malvinas ne a maimakon Farklands da Burtaniya da sauran kasashen duniya ke kiran tsibirin.

A shekara 1982 Argentina ta kwace tsibirin amma daga baya ta fice bayan wata yar gajeruwar yaki da aka yi mai muni da sojojin Burtaniya wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.