An jingine fille kan wani mutum a Saudiyya

Sarki Abdullah na Saudiyya
Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Wani babban jami'in gwamnatin Philippines ya ce Sarki Abdullah na kasar Saudi Arabia ya baiwa wani dan kasar ta Philippines wanda aka shirya aiwatar wa da hukuncin kisa a yau - karin watanni uku domin ya nemo dala miliyan daya da zai biya diyya.

Mataimakin shugaban kasar Jejomar Binay, ya ce Sarkin ya bai wa Joselito Zapanta wannan dama ne bayan da shugaban kasar Philippines Benigno Aquino ya gabatar da bukatar hakan.

An yanke wa Mr Zapanta hukuncin kisa ne bayan da ya kashe mai gidan da yake haya a ciki - sai dai idan har ya iya biyan kudin diyya ga iyalan mutumin, to za a yafe masa.

'Yan uwan Mr Zapanta sun ce kawo yanzu sun samu kashi daya bisa uku na kudin da aka bukata.