'Bai dace a yi wa Alamieyeseigha afuwa ba'

Tsoshon gwamnan jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha
Image caption Rahotanni sun nuna cewa Alamieyeseigha ya gudu daga Birtaniya sanye da kayan mata, abin da ya sha musantawa

A Najeriya tsohon shugaban hukumar EFCC, Mallam Nuhu Ribadu yace afuwan da aka yi wa tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Diepreye Alamieyeseigha koma baya ne, a yaki da cin hanci da rashawa.

Gwamnatin Najeriya ce ta baiwa tsohon gwamnan afuwa tare da wasu tsofaffin sojojin kasar.

Mallam Nuhu Ribado wanda a lokacinsa ne aka kama tsohon gwamnan tare da hukunta shi, ya ce matakin na shugaba Goodluck Jonathan ya sanyaya masa jiki matuka.

Kuma a cewarsa lamarin zai iya sanyaya jikin sauran jami'an da ke yaki da cin hanci a yanzu a kasar.

Tsohon gwamnan da ake wa kallon ubangida ne Mr. Jonathan, an taba kama shi da sama da fadi da miliyoyin daloli.

Amma yanzu shugaban kasar ya yafe masa wannan laifi, saboda a cewar mai baiwa shugaban kasar shawara, Doyin Okupe Alamieyeseighan ya yi nadama.

Afuwan da aka yi wa tsohon gwamnan na Bayelsa na nufin, zai iya tsayawa takarar kowanne mukami na siyasa, a kasar nan gaba.

An dai saki Alamieyeseigha a shekarar 2007, kwana biyu bayan kotu ta yanke masa hukuncin shekaru biyu a gidan yari.

A shekarar 2005 ne aka fara kama tsoshon gwamnan a Birtaniya , inda aka tuhume shi da laifin halatta kudaden haram, amma ya gudo Najeriya.