Boko Haram: Al'ummar Maiduguri na tsaka mai wuya

Image caption A lokuta da dama tituna na zama fayau saboda fargaba

Bisa dukkan alamu dai rigingimun da ake yi a kasar Mali na tasiri a kasar da ke gagara-badau din Yammacin Afirka ta fuskar soji da tattalin arziki wato Nijeriya.

Kungiyar gwagwarmaya ta Boko Haram na fafutikar kafa shari'ar musulunci, sannan ta soma tayar da kayar baya wa gwamnatin Nijeriya a 2009.

Bayan sace wasu Faransawa da ake garkuwa da su cikin watan jiya a kasar Kamaru, yanzu dai kungiyar na hakon 'yan kasashen waje ne domin samuwar gayya sabo day akin da ake yi a Mali.

Shugaban Nijeriya dai ya ziyarci Maiduguri, da ake wa lakabi da Gidan Boko Haram, a arewa maso gabashin Nijeriya a makon da ya gabata, inda ya shelanta cewa ba za a tsaigata wuta ba, a maimakon haka dubban dakarun hadin gwiwa da ya tura, zasu ci gaba da kasancewa a wajen.

Da wahala dai ka ga ana wasanni a birnin Maiduguri, yayin da makarantu kalilan ake da su a yankin na arewa maso gabashin Nijeriya da aka yi watsi da shi.

Karatu a Maiduguri

Wata makarantar ma ta kasance ta musamman ce, domin kuwa ta marayu da yara masu rauni ce. To amma filin da ya rage kankane ne, a cewar shugaban makarantar.

"A yau din nan da nake maka mgana, ina da sunayen yara marayu da basu gaza 150 ba, da kuma yara marasa galihu kamar 1006, wadanda ke son a sanya su a wannan tsari na makaranta.

Akwai dai matukar bukatar wurare a makarantu, domin kuwa a wajen makarantun akwa mummunar tayar da kayar baya.

Lamarin dai na raba yara da iyayensu, kuma sannu a hankali yana kassara birnin da a da ya kasance mai bunkasa.

Da dama dai na dora laifin tashin hankalin a kan kungiyar nan ta Boko Haram mai tayar da kayar baya.

Kisan gilla

Idan muka koma makarantar kuma, Salamatu mai shekaru goma sha biyu, ta yi bayanin abin da ya faru da mahaifinta.

"Da tsakar dare sai wasu mutane biyu maza suka shiga da karfi, kana suka finciko mahaifina daga cikin gidan sauronsa.

"Sai mahaifiyata ta soma addu'a, 'yar-uwata kuma tana kuka. Abin ba kyan gani. Mun yi tsammanin sun tafi da shi ne, amma a kashin gaskiya yankan rago suka yi masa, sannan kuma suka yi amfani da ruwan butarmu suka wanke wukar tasu.

"Mahaifiyata ta lullube gawar, washe-gari kuma dukkanninmu muka yi ta kuka" In ji Salamatu.

Gwamnatin Nijeriya dai ta tunkari lamarin ne ta hanyar girke Rundunar Tsaro ta Hadin Gwiwa, wacce wata babbar runduna c eta sojoji da 'yan-sanda da kuma jami'an liken asiri.

To sai dai kuma dirar mikiya da suke yi ta kasance mai muni.

Wata rana da dare a bara, sojoji sun zo neman mahaifin wata daliba 'yar shekaru goma sha biyu mai suna Fatima.

"Da dare, ina gidan kakana lokacin da sojojin suka fasa gidan namu da karfi suka shiga. Sun kama mahaifina tare da wasu mutanen sannan suka kashe su.

"Wasu lokutan nakan yi kuka yayin dana tuna shi." In ji Fatima.

To sai dai kuma mazauna birnin da daman na nuna tababa kan ko shin akwai ma lokacin da dakarun tsaron za su kashe wutar tayar da kayar bayan kuwa.?

Yaki da ta'adanci

A can Jihar Niger mai nisan dubban kilomitoci kuwa, rundunar sojin Nijeriya na kintsa yadda zata tunkari al'amarin.

Ana koyar sabbin dauka, dabarun yaki da ta'addancin ne, kuma sojin na kokarin shawo kan jama'a farar hula su amince su rika zakulo masu tayar da kayar baya da suka labe a yankunansu.

To sai dai a Maiduguri, mazauna birnin na zargin cewa sojojin na karya doka a wajen.

BBC ta ga wani gini da mazaunan ke cewa wata cibiya ce mai ban tsoro ta tsare mutane, wacce ake wa lakabi da Guantanamo.

Mahukunta dai sun nunar da cewa ana tsare da dubban mutane a ketaren gari, a Barikin Soji na Giwa na rundunar igwa ta 21.

Tsare mutane ba bisa ka'ida ba

Duk da kundin tsarin Mulkin Nijeriya da kuma Dokar Hana Ta'addanci sun bayyana karara cewa akwai bukatar a kai wadanda ake tsare da su gaban kotu cikin wani lokaci daidai kima.

A cewar daya daga cikin manyan lauyoyi na Maiduguri, ba a yin hakan.

"Doka cewa take yi cikin sa'o'I ashirin da hudu ko kuma arba'in da takwas. Idan aka ce lokaci daidai kima, to a ma ce mako guda.

"To amma yanu haka akwi mutane tsare a hannun rundunar JTF tun shekara ta dubu biyu da daya, har ya zuwa yau" In ji Lauya.

BBC dai ta tarar da masu dauke da makamai ne ke gadin babbar makabartar Maiduguri. Shaidu sun ce sun ga sun an sauke gawawwaki masu sutura kamar ashirin a babbar mota Tifa sannan aka zuba su cikin wani kabari na jam'i. Babu tabbacin yadda mutanen suka mutu, amma akai-akai akan yi irin wannan sauke gawawwaki.

To sai dai kuma shugaban rundunar sojan kasa ta Nijeriya, Azubuike Ihejirika, ya musanta cewa JTF na da hannu a duk wasu lamura na cin zarafin farar hula.

A fadin Nijeriya dai, da dama na nuna damuwa kan cewa idan fa ana ci gaba da samun masu fusata da hukumomi, to hala masu tayar da kayar baya su samu Karin sauki na daukar mutane aiki.

Karin bayani