Zaben Paparoma bai kaya ba

Image caption Dubban masu ibada sun taru domin ganin yadda za ta kaya

Bakin hayaki ya sake fitowa daga saman majami'ar Sistine a fadar Vatican, abinda ke nuna cewa an kasa cimma matsaya kan zaben sabon Paparoma a karo na biyu.

Cardinals da ke zaben sabon Paparoma sun shiga rana ta biyu a zaben da suke a cikin sirri a muja'mi'ar Sistine domin maye gurbin Paparoma Benedict wanda ya yi murabus a watan da ya gabata.

An rufe Cardinal-cardinal din su 115 a majami'ar ta Sistine har sai kashi biyu bisa ukunsu sun cimma matsaya kan zaben sabon Paparoman.

Za a ci gaba da kada kuri'a a ranar Laraba da yamma.

Manyan limaman za su ci rinka kada kuri'a sau hudu a kowacce rana har sai daya daga cikinsu ya samu kashi biyu bisa uku na kuri'un da za a kada.

Akwai dai wadanda ke tunanin cewa Cardinals din za su fuskanci kalubale musamman daga wadanda ke neman gaggarumin sauyi a darikar ta Katolika da kuma wadanda ke neman a ci gaba tafiya yadda ake.

Har wa yau akwai tunanin da wasu keyi cewa za'a dauki tsawon lokaci ba'a samu matsaya ba, wanda hakan zai iya nuna irin rarrabuwar kawunan da ake da shi a darikar ta Katolika.

Da zarar an kai ga zaben sabon Paparoman, to farin hayaki zai fito daga saman majami'ar ta Sistine.