Zaben Paparoma ya shiga rana ta biyu

Image caption Cardinals za su yi zabe sau hudu

Cardinals da ke zaben sabon Paparoma sun shiga rana ta biyu a yau a zaben da ke suke a cikin sirri a muja'mi'ar Sistine.

A yammacin jiya kuri'ar farko da su ka kada ya yi nuni da cewa ba su yi nasara ba saboda bakin hayaki ne ya fito daga mujami'ar.

A yau dai ana san ran za su yi zaben ne sau hudu.

Zaben rana ta farko da aka yi a jiya bai bada mamaki ba saboda dama ba'a a yi tunanin za'a cimma matsaya ba.

Bayan sa'o'i biyu ne bakin hayaki ya fito daga mujami'ar Sistine abun da ke nuni da cewa ba a samu matsaya ba kenan tsakanin Cardinals din.

Idan har farin hayaki ne dai aka gani, toh hakan nuni da cewa sun yi zabi sabon Paparoman.

A yanzu haka dai ba za a san wadanda su ke kan gaba ba a zaben rana ta farko da aka yi.

Cardinals din ne dai da kan su za su nemi mafita domin samu kuri'un da za su yi kashi biyu cikin uku.

Za'a zabe sau biyu ne da safen nan sannan kuma za'a kara yi sau biyu da rana.

Akwai dai wadanda ke tunaninc ewa Cardinals din za su fuskanci kalubale musamman daga wadanda ke neman gaggarumin sauyi a darikar ta Katolika da kuma wadanda ke neman a ci gaba tafiya yadda ake.

Har ya wau akwai tunanin da wasu keyi cewa za'a dauki tsawon lokaci ba'a samu matsaya ba, wanda hakan zai iya nuna irin rarrabuwar kawunan da ake da shi a darikar ta Katolika.