An samu wasu sinadarai a duniyar Mars

Image caption Motar Curiosity

Wata mota da aka tura duniyar watan Mars mai suna curiosity wadda ke tuka kanta,ta gano wasu sinadarai da ke nuna cewa a shekaru aru-aru da suka gabata akwai yiwuwar an samu wata halitta da ta taba zama a wajen.

Ita dai motar ta na nazarin wasu duwatsu da ta gano a watan da ya gabata.

Ta gano sinadarin Sulphur da sinadarin Nitrogeon da sinadin Hydrogen da sinadarin Oxygen da kuma sinadarin Carbon.

Masu binciken sun ce da wadannan sinadaran aka gano akwai yiwuwar za a iya samun halitta a wajen.

Mataimakiyar mai gudanar da binciken kimiyya ta cibiyar bincken NASA ta Amurka, Joy Crisp ta shaidawa BBC cewa;

Ta ce mun samu wani dutse,wanda da muka fasa kashi kashi ashirin zuwa talatin cikin dari na dutse na kunshe da ma'adini a cikinsa da sai an tace.

Wakilin BBC na kimiyya yace,wanna abu ne da ya bude wata hanya da nuna cewa wata halitta ta taba zamaa duniyar ta Mars.