Mario Bergoglio ne sabon Paparoma

Image caption Paparoma Francis

An zabi Cardinal Jorge Mario Bergoglio daga kasar Argentina a matsayin sabon Paparoma na darikar Roman Katolika.

Shi ne mutumin Latin Amurka na farko da ya zamo Paparoma.

Zai rinka kiran kansa Paparoma Francis 1 wato na daya.

Paparoma Francis yana da shekaru 76 da haihuwa.

Shi ne zai maye gurbin Paparoma Benedict XVI, wanda ya yi murabus a watan da ya gabata yana mai cewa bashi da koshin lafiyar da zai iya ci gaba da jagorantar cocin.

Sa'a guda kafin haka, farin hayaki ya fito daga saman majami'ar Sistine, wanda ya nuna cewa manyan limaman sun zabi sabon Paparoman.

Dandazon mutanen da suka taru a dandalin St Peter sun rude da ihu sannan kararrawa ta kada a lokacin da hayakin ya fito.

Takaitaccen tarihin Paparoma Francis

Cardinal Bergoglio wanda a ya zabi sunan Paparoma Francis na farko.

A rayuwarsa ta aiki a Argentina, ya dukkufa ne wajen tabbatar da ganin an samu daidaito a al'umma da kuma ganin a kare hakkokin talakawa.

A kasar Argentina mabiya darikar ta katolika sun jinjinawa zaben na shi.

Mutane da dama dai ba su sanya shi cikin rukunin wanda za'a iya zabe a matsayin Paparoma, amma a zaben da aka yi a baya da ya fito da Paparoma Benedict shine ya zama na biyu.

Ana dai girmama shi saboda illiminsa. Ya kuma yi karatun addini ne a Jamus kuma ya yi zauna a kasar Italiya.

Paparoma Francis zai kawo wani sabon salo ga shugabancinsa saboda shine Paparoma na farko dake darikar Jesuit ta Katolika.

Ya dai jagoranci al'ummar Katolika a Argentina a lokacin mulkin soji, lokaci da mutane da dama suke cikin ukuba a kasar, amma akwai wanda suke sukarsa a wannan lokacin da cewa bai fito ya kalubalanci gwamnatin kasar ba.

Sabon Paparoman yana da ra'ayin mazan jiya ne, kuma yana adawa da lallata da auren jinsi daya da kuma zub da ciki.

Ganin irin gudunmuwar da ya bayar wajen ganin a samu daidaito a Argentina , ana ganin Cardinal Bergolgio zai ci gaba da ayyukan wanda ya gada ne na kokarin ganin ya hada kan al'ummar Katolika da kuma tabbatar da aldalci a duniya.

Amma ganin yadda wasu al'ummar Katolika ke juyawa cocin baya a wasu kasashen Turai, saboda matsalar lallata da kananan yara, Sabon Paparoma Francis na farko na da babban Kalubale a gabansa.

Karin bayani